Connect with us

News

Putin ya soke shirin kai hari a masana’antar karafa ta Azovstal a Mariupol

Published

on

Daga Kabiru basiru fulatan

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci sojojinsa su fasa kai hari a masana’antar mulmula karafa ta Azovstal da ke birnin Mariupol da aka yi wa kawanya, yana mai cewa yana son a ci gaba kare ta.

Mayakan Ukraine na karshe a birnin sun buya a masana’antar, kuma rahotanni sun akwai fararen-hula kusan 1,000 da ke cikin mawuyacin hali a can.

Putin ya bayar da umarnin rufe masana’antar yayin tattaunawar da ya yi da Sergei Shoigu, ministan ma’aikatar tsaron kasar, wadda aka watsa a kafafen labarai.

Ya taya kansa murna bisa nasarorin da suka samu a Mariupol bayan Shoigu ya yi ikirarin cewa dakarun Rasha sun kwace birnin.

A baya Shoigu ya shaida wa Putin cewa akwai fiye da mayakan Ukraine 2,000 a cikin masana’antar, wadanda suke cikin dakunan karkashin kasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending