News
Buhari ya yi jaje kan mutuwar sojojin saman Najeriya
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jajen mutuwar sojojin Najeriya biyu wadanda suka yi hatsarin jirgin saman soji a Kaduna da ke arewacin kasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu, ya fitar ya ambato Shugaba Buhari yana bayyana “damuwarsa” bisa mutuwar Flight Laftanar Abubakar Alkali da Flight Laftanar Elijah Haruna Karatu.
“Na yi matukar kaduwar da ba zan iya cewa komai ba bisa rasuwar wadannan matasa biyu wadanda suka sadaukar da rayuwar wajne bauta wa kasa,” in ji Buhari.
Ranar Talata ne jirgin rundunar sojin sama ta Najeriya ya yi hatsari inda duka jami’an biyu da ke cikinsa suka mutu.
A cikin shekara guda da ta gabata dai, jiragen sojin saman Najeriya na yawan faduwa, lamarin da ke sanadiyar mutuwar jami’an sojin.
