Hukumar da ke yaki da masu tu’ammalli da miyagun kwayoyi NDLEA ta kama wasu ‘yan Najeriya masu safarar hodar Ibilis ta hanyar boye su a wurare kamar cikin ganyen shayi.
Hukumar ta ce ta kama akalla masu safarar hodar ta Ibilis mutum hudu yayin da suke kokarin shigowa da fitar da its Najeriya a makon jiya.
A halin yanzu suna hannun hukumar, kuma ana gudanar da bincike, kamar yadda jami’i mai hulda jama’a na hukumar, Femi Babafemi ya shaida wa manema labarai.
Ya ce sun damke daya daga cikinsu mai suna Pascal Ekene Okolo yayin da ya iso Najeriya cikin jirgin saman Qatar daga Sao Paolo a ranar Lahadi 17 ga wannan watan.
Mista Okolo ya sanar da NDLEA cewa shi mai sana’ar maganin gargajiya ne kuma bayan da aka binciki kayansa, an gano kayan shayi da aka hada ganyayyaki, wanda a ciki aka boye kilo 4.1 na hodar Ibilis.
A wannan ranar kuma hukumar ta kama wani dan Najeriya mazaunin kasar Kanada mai suna Anigo Christian Godspower a fili jirgin saman Legas wanda shi ma ya iso Najeriya daga Sao Paolo na Brazil kuma ya yada zango a biri Doha na kasar Qatar.
NDLEA ta gano yana dauke da hodar Ibilis da nauyinta ya kai kilo 2.1.
