Connect with us

News

An yi bikin ranar ma’aikata ta duniya

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

 

 

 

Ranar Lahadi aka yi bikin ranar ma’aikata ta duniya, wanda aka saba gudanarwa a duk ranar 1 ga watan Mayu a kasashe daban daban.

Dubun dubatar masu zanga-zanga a sassan duniya sun mamaye tituna don bikin wannan rana, tare da matsa lamba ga hukumomi wajen ganin sun inganta ‘yancin ma’aikata.

Advertisement

Hotunan da ke yawo a kafafen yanar gizo sun nuna yadda dubban mutane suka yi gangami a kasar Sri Lanka, da Turkiyya, da India da Pakistan, har ma da Girka, da Faransa da dai sauran kasashe da dama.

Masu bikin ranar ma’aikata ta duniya a birnin Paris.
Masu bikin ranar ma’aikata ta duniya a birnin Paris. AP – Lewis Joly
Jama’a da kungiyoyin kwadago a biranen nahiyar Turai sun fito kan tituna domin gudanar da jerin gwano tare da sakonnin bukatu ga gwamnatocinsu, musamman a kasar Faransa inda aka yi amfani da hutun na karrama ma’aikata a matsayin lokacin gangamin nuna adawa da sabon shugaban kasar Emmanuel Macron da ya sake lashe zabe.

A Turkiya, ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun kame masu zanga-zangar da dama da suke kokarin isa dandalin Taksim na Istanbul don gudanar da gangamin nuna adawa da matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kaya ya haifar.

A Najeriya

Wasu daga cikin yayan kungiyar kwadago sun rasa rayukansu a sakamakon harin yan Bindigan Kaduna

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya bayyana cewa ma’aikata 36 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin yan bindiga a Jihar.

Advertisement

Dalilin da ya sanya a wajen taron bikin yayan kungiyar kwadagon domin murnar ranar bikin ma’aikata ta duniya aka yi shuru na minti daya domin tunawa da wadanda suka rasu sabili da matsalar rashin tsaron.

Ayuba Magaji da yake jawabi a wajen taron ranar ma’aikata ta shekarar 2022 a babban filin wasa na ABS da ke Kaduna ranar Lahadi ya yi kira ga ma’aikatan dasu tabbatar sun mallaki katin zabe domin fitar da duk wani dan siyasa da ba zai kare miradunsu ba.

Shugaban kungiyar kwadago ya kuma bukace su, da su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa gadan gadan a madadin su tsaya a matsayin yan Kallo.

Ayuba Magaji ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa irin yadda take gudanar da aikin gine ginen tituna da sauransu musamman a garuruwan Kaduna Kafanchan da Zariya, Sai dai ya ce samar da shugabanci nagari ya wuce irin yadda ake yin aikin a halin yanzu don haka ake bukatar a yi aiki tukuru ta fuskar shigar da al’umma a cikin tafiyar da Gwamnatin samar da Adalci.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta canza irin salon tsohon yayin gudanar da dangantaka tsakanin ta da kungiyoyin kwadago wanda hakan zai ba ta damar tafiya da zamani kamar yadda ake yi a duniya ta hanyar tattaunawa da ma’aikata a duk abin da za ta gudanar a tsakaninsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending