Connect with us

News

Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmi, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto ran Lahadi.

Published

on

Daga maryam Bashir musa

 

 

 

Wasu al’umma mabiya Addinin Musulunci a Sokoto sun gudanar da Sallar Eid-El-Fitr jiya Lahadi inda suka saba wa umarnin Sarkin Musulmai Mutanen waɗan da mafi yawancin su mabiya Shekih Musa Lukwa ne, sun yi Sallah da misalim ƙarfe 8:00 na safe bayan tabbatar da ganin wata

Sheikh Lukwa ya bayyana cewa mutane da dama sun ga jinjirin watan Shawwal a sassan Sokoto da wasu kasashen waje

Advertisement

Wasu Musulmai a jihar Sokoto sun gudanar da Sallar Idi yau Lahadi wanda ya saɓa wa umarnin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Eid-ul-Fitr. Daily trust ta rahoto cewa a ranar Asabar, Sarkin Musulmai ya sanar da cewa ba’a ga jinjirin watan Shawwa 1443AH ba a sassan Najeriya.

Mafi yawan Musulman, waɗan da mabiya ne ga Sheikh Musa Lukwa, sun gudanar da Sallar idi wato ƙaramar Sallah da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi. Da yake zantawa da wakilim jaridar, Sheikh Lukwa, ya ce sun samu sahihan bayanan ganin jinjirin watan Shawwal a wasu sassan Najeriya da wasu ƙasashen waje.

A jawabinsa, yace Musulmai sun ga wata jihohi biyar na Jamhuriyar Nijar, inda ya ƙara da cewa: “Na kalli bidiyon shugaban ƙasar su (Nijar) lokacin da yake ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar idin ƙaramr Sallah, kuma an ga wata a ƙasar Afghanistan, Mali da wasu ƙasahen Afirka kuma sun gudanar da Sallah yau.” “A nan Sokoto, Mutum Takwas sun tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a ƙauyen Fakku da ke ƙaramar hukumar Kebbe, cikinsu har da babban limamin su.”
“Haka nan mutum 50 sun tabbatar da ganin jinjirin wata a ƙauyen Wauru. ƙaramar hukumar Gada duk a nan jihar Sokoto.”

Legit.ng Hausa ta samu zantawa da ɗaya daga cikin mabiyan da suka gudanar da Sallah wanda ya bayyana sunnasa da Nisfu Hayat, ya shaida mana cewa matsalar ganin wata a Najeriya ba yau aka fara ba. Hayat wanda ya ayyana yau a matsayin ranar Sallah a wajensa ya shaida wa wakilin mu cewa: “Gaskiya matsalar ganin wata a Najeriya tana da girma zan iya cewa Sarkin Musulmi ne ya assasa ta, ba shi ne basarake na farko ba, wasu sun gabace shi amma shi aka fara samun matsala da shi.” ”

Abun da son rai a ciki, anan Sokoto kowa ya san akwai wani Malami da ya fito ya ce ya bar kwamitim duban wata domin akwai matsala a ciki.”

Shin meyasa Sheikh Lukwa ya ɗauki wannan matakin?

Advertisement

Ya ƙara da cewa Sheikh Lukwa Malaminsa ne da yake bin Sunnah, kuma tun ba yanzu ba yake kai korafi kan ganin wata ga Kwamiti amma ba’a duba wa.

Ya shaida mana cewa: “Malam Musa Lukwa malami ne mai bin aƙidar magabata (Salaf), yana kai korafe-korafe idan an ga wata yana sanar da Sarki amma ba’a dubawa, dalilin shi ne sun maida ganin watan a kimiyyance.” “Mun yi Sallah yau saboda an ga wata a Nijar, an ganshi a wasu sassan Najeriya har da nan Sokoto.”

Hakazalika

Yan Sanda Sun Cafke Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Idi A Sakkwato

‘Yan sanda sun cafke babban Limamin nan da yayi sallar Idi ayau Lahadi a karamar hukumar Gada a jihar Sakkwato.

Limamin dake wani gari da ake kira da Dantudu, ya bayyana cewa ya umurci mabiyansa da su sha ruwa su ajiye azumin Ramadana biyo bayan tabbacin ganin jaririn watan shawwal da yace angani.

Advertisement

Ranar Litinin Ita Ce Ranar Karamar Sallah A Nijeriya
Sabida wannan danyen hukuncin nayin Sallar Idi shi da Mabiyansa, uban kasar Gada yasa aka tasa keyar malamin Zuwa fadarsa domin ya amsa wasu tambayoyi.

Cikin Tambayoyin da Masautar Tayi wa Malamin Kamar yadda jaridar alfijr ta wallafa ta ce, masarautar ta tambaye malamin kan cewa shike da Ikon Fadar Anga Watan Shawwal ko Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ada Abubakar?

Limamin ya Amsa da Cewa “Shi Malamin da Yayi Karatu a Wajen ya Gaya Masa Matukar ya Sami tabbacin anga Wata to yana iya ajiye Azuminsa yayi Sallah, Tuni Dai Al’ummar da Suka Karbi Fatawar Malamin Suka Ajiye Azumi Sun Garzaya a Fadar Mai Alfarma Uban Kasar Gada Wasu Rike da ‘Pure Water’ da Biskit da Kayan Ciye_Ciye Suna Bukatar a Sallami Malamin.

A wani labarin kuma mun kawo yadda aka gudanar da Sallar Idi ƙarama a jamhuriyar Nijar biyo bayan ganin wata da mhukunta suka sanar a ƙasar A ran Lahadi, 1 ga watan Maris ne al’ummar Musulmi suka yi sallar idi a Jamhuriyar Nijar bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a kasar, lamarin da ya kawo karshen azumin Ramadana.

Ba a yi sallah ba a kasashe da dama ciki harda Saudiyya da Najeriya sakamakon rashin ganin wata. Hakan na nufin sai yau Litinin za a sallaci idi a kasashen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending