Connect with us

News

An sace mutane ‘da dama’ a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

Rahotanni daga Najeriya na cewa masu garkuwa da mutane sun sace mutane da dama a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata.

Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Katari da misalin 4:30 na yammaci.

‘Yaran da ke fama da yunwa na ci gaba da karuwa’

Advertisement

Ya bayyana cewa akwai motoci da dama waɗanda suna ajiye a kan ɓangaren zuwa Kaduna da ɓangaren dawowa da aka yi awon gaba da masu motocin.

Ya kuma ce bayan faruwar lamarin jami’an tsaro masu ɗumbin yawa sun isa wurin domin kai ɗauki.

BBC ta tuntuɓi gwamnatin Jihar Kaduna da kuma rundunar ƴan sadan Najeriya reshen Kaduna domin jin ƙarin bayani, sai dai dukansu ba su ɗaga wayoyinmu ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending