Connect with us

News

Buhari zai tafi Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta United Arab Emirates (UAE) a yau Alhamis.

Buhari zai gana da sabon Shugaban Ƙasa Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan a birnin Abu Dhabi don yi masa ta’aziyyar tsohon Shugaban Ƙasa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, a cewar wata sanarwa daga Fadar Shugaban Najeriya.

Kazalika zai taya sabon shugaban murna da kuma “sabunta ƙawancen da ke tsakanin Najeriya da UAE na tsawon shekaru”.

Advertisement

Ministocin da za su yi wa Buhari rakiya sun haɗa da Ministan Sadarwa Isa Pantami, da Ƙaramin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada, da Ministan Sufurin Jirgin Sama Hadi Sirika, da Ministan Abuja Mohammed Bello.

Ana sa ran zai koma gida Najeriya ranar Asabar.

Social embed from twitter

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending