Connect with us

News

Zargin danne wa kananan sojoji hakkinsu a Najeriya na iya zama gaskiya – Bincike.

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

 

Yayin da hukumomin sojin Najeriya suke watsi da wani zargi da kananan sojoji ke yi wa manyansu na tauye musu hakkoki, wadansu bayanai da BBC ta samu na cewa akwai lokutan da ake samun jinkirin biyan kudaden alawus, kuma idan ba a yi sa’a ba sun makale ke nan.

An Haramta Acaba A Wasu Sassan Birnin Legas ‘Har Abada’

Advertisement

Masana sha’anin tsaro dai na cewa rashin biyan hakkokin jami’an tsaron, na iya sanyaya gwiwar sojojin da ke fagen fama.

Wadansu kananan sojoji ne suka rubuta budaddiyar wasika ga shugaba Buhari suna zargin cewa ana cinye musu kudadensu na alawus.

A martanin da ta mayar dangane da zargin danne hakkin kananan sojojin, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ana biyan jami’an ne ta wani tsari na asusun bai-daya.

Ta ce a bisa wannan tsari ba ta yadda za a ware wani soja a yi masa kwange a kudinsa na alawus.

To amma a binciken da BBC ta yi ta gano cewa kananan sojojin suna korafi ne kan kudaden alawus da ake ware musu na kwanan daji, a lokacin da suke bakin-daga, idan an tura su aiki.

Wani soja da BBC ta tattauna da shi, ta sirri ya ce, ana biyansu naira dubu 45 ne a duk wata, idan suna bakin-daga.

Advertisement

Sai dai ya ce inda Gizo ke sakar shi ne, wajen biyan musamman ma idan kana sabon zuwa kamar yadda ya ce: ”To amma a dubu 45 din sai ka ga ka zo sabo-sabo nan ne aka fi samun matsalar.”

”Sai ka ga ka yi wata biyu, uku wani ma ya kai biyar ba ya samunsu.” In ji shi.

Ya ce a irin haka ana tara sunayen sai kwamandan ya ce ku tattara sunayen wanda ya san yana da matsalar biya.

Daga nan kuma sai ku jira idan mutum ya yi sa’a sai ka ga abin ya fara aiki.

”Ni nawa an rike min wajen wata hudu haka amma sauran duka sun biya ni da suka bude.

“Sai da na yi wajen wata biyar to a wata na biyar din sai suka fara biya na to wancan wata hudu da suka wuce duka ba su ba ni ba.” In ji sojan.

Advertisement

Dangane da kayan sarki kuwa, sojan ya ce a yanzu ba a ba su sai dai su saya, amma a da ana raba musu ne.

Sai dai kuma jami’in ya ce galibi kyautata wa ko akasin haka, abin ya dogara ne ga kwamandanku, kasancewar wasu masu kirki ne wasu kuma marassa kirki ne.

To amma kuma ya ce a yanzu rayuwar sojojin ta fara inganta tun bayan da aka nada sabon hafsan sojin kasa na yanzu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending