Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Lewandowski, Depay, Pogba, Dybala, Depay da Mbappe

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

Advertisement

Dan wasan Paris St-Germain Kylian Mbappe zai sanar da matakinsa game da makomarsa a ranar Lahadi. An dade ana alakanta dan wasan na Faransa mai shekara 23 da komawa Real Madrid. (L’Equipe)

Paul Pogba ya amince da yarjejeniyar sirri da Manchester City amma ya ki amincewa da komawa Manchester United saboda dan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara 29, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara, ya damu da sukar da yake sha daga magoya bayan United (Times)

Har yanzu tsohuwar kungiyar Pogba ta Juventus, na fatan dawo da dan wasan, baya ga kokarin da suke yi na daukar dan wasan tsakiyar Italiya Jorginho, mai shekara 30, daga Chelsea. (Gazzetta dello Sport)

Arsenal, da Newcastle da Everton na zawarcin dan wasan gaban Barcelona Memphis Depay, mai shekara 28. (Sport)

Advertisement

 

Dan wasan gaban Argentina Paulo Dybala ya ce ba zai koma Tottenham ba yayin da dan wasan mai shekara 28 ke neman kungiyar da zai koma, bayan ya tabbatar da cewa zai bar Juventus a karshen kwantiraginsa a bazara. (AS)

Tottenham kuma tana sha’awar siyan dan wasan bayan Faransa Clement Lenglet, mai shekara 26, wanda ke da ‘yancin barin Barcelona. (Sport)

Robert Lewandowski na Bayern Munich na son komawa Barcelona, inda aka tattauna kan sanya hannunsa har zuwa 2025, duk da cewa har yanzu dan wasan na Poland mai shekara 33 bai yi magana da wata kungiya ba. (Fabrizio Romano)

Advertisement

 

An bai wa Manchester United damar sayen dan wasan baya na Barcelona na Amurka Sergino Dest, mai shekara 21. (90Mint)

Dest na iya zama wanda zai maye gurbin dan wasan bayan Ingila Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 24, wanda za a bar shi ya bar United a bazara. (Sky Sports)

Da alama United tana gab da hakura da dan wasan Ajax da Netherlands Jurrien Timber, inda dan wasan mai shekara 20 ya yi watsi da batun sauya lambar da yake bugawa (Sun)

Advertisement

 

Divock Origi na shirin komawa AC Milan lokacin da kwantiraginsa da Liverpool zai kare a bazara, inda dan wasan gaban na Belgium, mai shekara 27, ke jiran a duba lafiyarsa. (Guardian)

Arsenal ta shirya tsaf domin siyar da dan wasan gaban Ivory Coast Nicolas Pepe, mai shekara 26, wanda suka saya a kan kudi fam miliyan 72 a shekara ta 2019 (Football Insider)

Tsohon dan wasan baya na Manchester City Vincent Kompany na cikin manyan masu takarar neman kocin Burnley, sai dai aikinsa da kungiyar zai yiwu ne idan kungiyar ta tsira daga faduwa daga gasar Premier a bana (Manchester Evening News)

Advertisement

 

Juventus ba za ta rike dan wasan gaban Sifniya Alvaro Morata mai shekara 29 dindindin ba, dan wasan da ya shafe shekara biyu a matsayin aro daga Atletico Madrid. (Marca)

Manchester United ta soke kyautar gwarzon dan wasan da take yi duk shekara saboda ‘yan wasan suna jin kunyar halartar irin wannan taron bayan kasa tabuka abin kirki a halin da ake ciki (Mirror)

Newcastle United za ta fara tattaunawa da Eddie Howe kan sabon kwantiragi a bazara a matsayin tukuicin kaucewa faduwa daga gasar Premier. (Mail)

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *