Connect with us

News

Dan Takarar Da Ke Hannun ’Yan Bindiga Ya Lashe Zaben Fid Da Gwanin PDP A Kaduna

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

Dan Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) Sadiq Ango Abdullahi, ya lashe zaben fid da gwanin dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Sabon Gari a Jihar Kaduna, duk da cewa har yanzu yana hannun ’yan bindiga.

Gwamna Ganduje ya raba naira miliyan goma sha shida ga iyalan wadanda fashewar Bom ya shafa a Sabon Gari.

An dai sace shi ne tun lokacin da mahara suka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari, sannan suka sace mutane da dama.

Advertisement

Sadiq dai ya sami kuri’a 28 yayin da sauran ’yan takarar suka biyo baya.

Sauran ’yan takarar, Hadiza Muhammad, da kuma Misis Paulina, Salisu Abdulhamud suka sha kaye a zaben.

Idan za a iya tunawa tun a ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2022 ’yan bindigar suka yi awon gaba da shi da wasu matafiya a jirgin kasa.

Tun a lokacin ba a sake jin duriyarsa ba a fagen siyasan ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending