Connect with us

News

Ciyar Da ‘Yan Makaranta: Gwamnati Za Ta Kashe N999m Kullum Don Ciyar Da Ɗalibai 10m.

Published

on

Daga Maryam bashir musa

 

 

 

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta kashe Naira miliyan 999 a kowacce rana karkashin shirinta na ciyar da yan makarantun frimare don ciyar da kimanin dalibai miliyan 10 a kasar.

Jagorar shirin, Hajiya Aishatu Digil ce ta sanar da hakan a ranar Talata a Abuja, wurin taron masu ruwa da tsaki kan hanyoyin da za a bi don aiwatar da shi.

Advertisement

A cewarta, Ministan Jinkai da Walwalar Al’umma, Hajiya Sadiya Farouk ta samu amincewar kashe N100 kan ciyar da kowanne dalibi/daliba a makaranta a kullum.

Ta ce za a fara ciyar da yan aji daya zuwa uku na frimare su kimanin 9,990,862 da abincin N100 a kullum, kudin zai kama N999,086,200.

“A baya, muna kashe N70 don ciyar da kowanne dalibi a rana tun shekarar 2016, amma shugaban kasa ya amince a kara kudin zuwa N100.

“Muna tare da masu ruwa da tsaki kaman Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kididdiga ta Kasa da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa, NOA, da Ma’aikatar Noma da ta Ilimi don tattauna hanyoyin kasafta kudaden.

Ɗan Namadi Sambo ya nemi a dawo masa da kuɗaɗensa bayan shan kaye a zaɓen fidda-gwani

“Mun zo nan domin duba hanyar da za a fi samun amfani a shirin bisa sabuwar karin kudin da aka samu domin inganta yanayin abincin da aka bawa yara, in ji ta.

Advertisement

Ta cigaba da cewa “Ga yadda za a kashe Naira 100; N70 shine kudin abincin baki daya amma banda kwai, N14 shine kudin kwai da za a aiwatar da hannun hadin gwiwa da Kungiyar Masu Kiwon Kaji na Najeriya.

“Muna shirin samar da ‘Larabar Kwai’ inda kowanne dalibai za a rika bashi kwai guda daya ranar Laraba.

“N10 kudin masu dafa abinci ne, N11 kuma kudin sinadaran girki sai N1 kuma ta masu kula da ingancin abincin, amma ba dole ba ne.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending