News
Shugaba Buhari ya samu lambar yabon mai gaskiyan duniya kuma jagoran yaki da rashawa.
Daga yasir sani Abdullah
Kungiyar masu binciken kwa-kwaf na Forensics na Najeriya watau Chartered Institute of Forensics and Certified Fraud Examiners of Nigeria (CIFCFEN) ne suka gabatar masa da wannan lambar yabo.
A cewarsu, sun bashi ne don jinjinawa kokarin da yake yi wajen yaki da rashawa da kuma jajircewarsa wajen yiwa yan Najeriya aiki.
Ciyar Da ‘Yan Makaranta: Gwamnati Za Ta Kashe N999m Kullum Don Ciyar Da Ɗalibai 10m.
A jawabin da mai magana da yawin Buhari, Mr Femi Adesina, ya fitar, ya ce Shugaban majalisar amintattun CIFCFEN, Dr Iliyasu Gashinbaki, ne ya gabatar da lambar yabon ranar Talata a Abuja, rahoton Vanguard.
A cewarsa, babu wanda ake ba wannan lambar yabon illan shugabannin kasashen Afrika masu hali na kwarai. Yace Shugaba Buhari ne shugaban kasa a nahiyar Afrika na farko da aka ba wannan lambar yabo.
Ya ruwaito shugaba Buhari na cewa: “Wannan karramawa na kara min karfin gwiwan cewa mu yan kasar nan zamu iya abinda ya dace don kuma kwaikwayon halayen magabatanmu.”
Buhari ya jinjinawa mambobin kungiyar bisa kokarin da suke wajen taimakawa kungiyoyin yaki da rashawa irinsu EFCC, CCB, ICPC da hukumar yan sanda.
Shugaban ya yi musu alkawarin rattafa hannu kan dokar majalisa dake kan teburinsa wacce ke tabbatar da kungiyarsu a hukunmance.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
