Connect with us

News

Kisan da ake yi wa ‘yan Arewa a Kudancin Najeriya ya isa haka- -CNG

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

IPOB na sake zama barazana ga ‘yan Arewa da ke zaune a kudancin Najeriya

Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula a Arewacin Najeriya sun ja hankalin Shugabannin Arewaci da na Kudanci da kuma gwamnatin tarayya, da su dauki matakin kawo karshen kashe-kashen da ake yi wa ‘yan asalin Arewacin kasar da ke harkokinsu a Kudu Maso Gabashin kasar kafin lokaci ya kure.
Wannan na zuwa bayan da a farkon mako wasu ‘yan bindiga suka kashe wata mata mai suna Harira da ‘ya’yanta hudu da kuma wasu yan Arewacin kasar da ke sana’o’i a jihar Anambra.

Advertisement

Mijin matar kuma mahaifin ƴaƴan dukkanin mata da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe matarsa ne da ƴaƴansa a lokacin da suke kan hanyar dawo wa daga ziyarar da ta kai, tare da ƴaƴanta a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.

“Na shiga tashin hankali, saura kaɗan na haukace – kamar an saka ni cikin wuta, haka nake ji saboda zafin da nake ji,” in ji Jibril Ahmed mijin matar da aka kashe da kuma ƴaƴansa huɗu.

“Yanzu ina zan fara – yaya zan yi aure har na samu ƴaƴan da Allah ya ba ni waɗanda har sun yi nisa da karatu.”
“Yarana suna da basira amma ga shi yanzu irin ɓarnar da aka yi min, kawai na yi tawakalli ga Allah – Allah zai saka min,” in ji shi.
Bayan haka kuma maharan sun kona tirelolin dakon kaya da rahotanni basu ce ga adadinsu ba duk dai a jihar ta Anambra.

A hira da BBC Shugaban kungiyar ta CNG Nastura Ashir Shariff ya ce ci gaba da kyalewa ko yin ko oho da kisan al’ummar Arewa da ke zaune Kudancin Najeriyar zai iya zama wani abun da na sani ga Shugabannin, don kuwa idan basu dauki mataki cikin gaggawa ba lokaci zai kure musu.
”Tun daga 2017 suke kashe mutanen Arewa mazauna yankunan su. Mun sha fitowa mu yi kira ga mutanen Arewa cewa ka da su dauki doka a hannu, kar su dauki martani ga irin kashe-kashen da aka dinga yi musu.”
”Amma yanzu tun da suke kashe mutanen nan baka ji wani babba a Arewa ya fito ya fito ya yi magana ba.”
Amma da Arewa ne wani abu ya faru da yanzu ka ji sun fito sun fara magana suna cewa an dau doka a hannu.” In ji Nastura Ashir Shariff.
A kan haka kungiyar ke ganin mafita daya ce, wato a kyale mutanen Kudancin kasar su balle kamar yadda suke bukata, don a cewar Shugaban na CNG babu wata gwamnati da za a kafa a gabar da ake ciki da za ta iya magance wannan matsala.
Kisan Harira da ya’yanta hudu mata a jihar Anambra da ake zargin kungiyar IPOB da aikatawa ya fusata yan Arewacin Najeriya.

Lamarin ya janyo tada jijiyar wuya a shafukan sada zumunta, inda da dama ke sukar gazawar gwamnati, da kuma yadda Shugabannin Arewacin kasar da sauran masu fada a ji suka yi gum da bakinsu, kamar basu san me ya faru ba a cewar wasu masu amfani da shafukan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending