News
Za a kashe wani dan kasar Denmark da ya kashe matarsa ‘yar Najeriya
Daga Maryam Bashir Musa
Kafar VOA Hausa ta wallafa yadda wata kotu ta yanke hukuncin kisa ga wani dan kasar Denmark da aka kama da laifin kashe ‘yarsa da matarsa ‘yan Najeriya. Kafar ta bayyana cewa “Wata babbar kotun jihar Legas ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani dan asalin kasar Denmark da aka samu da laifin kashe matarsa da diyarsa ‘yar shekaru 3 da rabi.
Shekara hudu da suka gabata ne dai ‘yan sanda suka kama Peter Nielsen, dan shekaru 54 a duniya da laifin kashe matarsa mai suna Zainab da ‘yarsa Petres a gidansu da ke Legas.
Kotu ta ce bisa hujjojin da ke gabanta na ‘yan sanda masu bincike da na likita ya nuna cewar Peter ne ya shake su har suka mutu, don haka hukuncinsa shi ne hukuncin kisa ta hanyaR rataya.
Masu fafutukar kare hakkin bil’adama da dama ne dai suka matsa wajen ganin an hukunta Peter duk da cewar ba dan Najeriya ba ne, amma kuma a Najeriya ya aikata laifin.
Dr Joy Odumakin mai fafutukar kare ‘yancin mata a Najeriya na daya daga cikinsu da ta yaba da hukuncin kotun bayan shariar shekaru hudu, kamar yadda ta shedawa ‘yan jarida a harabar kotun a Legas.
Yanzu haka dai ‘yan najeriya da dama ne dai ke zaman hukuncin kisa a gidajen yarin Najeriya ba tare da gwamnonin da doka ta amince da sanya hannunsu kafin aiwatar da hukunci ba, ke kin sanya hannun, don haka a karshe ake bigewa da tamkar hukuncin daurin rai da rai ne aka yanke.
Sai dai yanzu abun jira a gani shi ne ko Denmark za ta bukaci musayar fursuna tsakaninta da Najeriya domin ba da dama a mai da dan Denmark din kasarsa ta asali.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
