News
Gawuna Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Gwamna a Jami’yyar APC.
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya lashe zaben fidda gwani na takarar zama gwamna a karkashin jam’iyyar APC.
Da yake sanar da sakamakon, shugaban kwamitin zaben Sanata Tijjani Yahaya Kaura yace Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya samu ƙuri’u 2289, yayin da Honorable Sha’aban Ibrahim Sharada ya zo na biyu da ƙuri’u 30.
Sake gina Borno ya fi min zama mataimakin shugaban kasa – Zulum
Zaben ya samu halartar wakilan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da jami’an tsaro da kuma mambobin jam’iyyar ta APC.
Dr Nasiru Yusuf Gawuna dai ya samu goyon bayan gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna.
Advertisements
