Connect with us

News

Kudan Zuma Sun Sanadiyyar Mutuwar Wani Yaro Dan Shekara 13 A Jihar Kano

Published

on

Daga Khadija abdullahi muhmd

 

 

Wasu gungun kudan zuma sun kai hari tare da yin sanadiyyar rasa ran wani yaro dan shekara 13 mai suna Ismail Hussaini a kauyen Yanoko dake karamar hukumar Tofa a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a makarantar Firamare ta Nomadic ta Yanoko yayin da dalibai ke cikin azuzuwansu.

Dagacin kauyen Yanoko, Habibu Bello ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.

Advertisement

Ya bayyana cewa an garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibiti inda ya rasu a lokacin da ake kula da lafiyarsa.

Sunusi Bature Dawakintofa, wanda na kusa da marigayin ne, ya shaida wa manema labarai cewa, an kai wa mamacin harin ne biyo bayan kasa guduwa da ya yi saboda cutar da ya ke fama da ita a sakamakon ciwon sikila.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending