Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa hukumomin bayar da agaji a Jamhuriyyar Nijar sun kasa jure wa kwararar yan gudun hijira da ke shiga ƙasar.
Majalisar ta ce akasarinsu na zuwa yankunan da ke fama da ƙarancin abinci.
Sama da ƴan gudun hijira dubu 36 ne suka shiga Nijar a watanni huɗu na bana – akasarinsu farar hula ne masu guje wa yaƙin masu iƙirarin jihadi a makwaftan ƙasashe.
Ita kanta Nijar ɗin na fuskantar hare-haren masu iƙirarin jihadi. Wani wakilin hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Emmanuel Gignac ya bayyana cewa wasu daga cikin ƙananan yaran da ake gudun hijira da su na fama da matsalar abinci mai gina jiki.
Ya yi kira da a bayar da agajin gaggawa domin samar da kayayyakin kiwon lafiya da kuma ilimi.
