Dan majalisar tarayya na karamar hukumar Birni, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya zargi gwamnatin Kano da kai masa farmaki a lokacin zaben fidda gwani na dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC, wanda ya gudana a daren jiya Alhamis, a rufaffen dakin taro dake filin wasa na Sani Abacha, wanda yace daƙyar yasha domin an bukaci a kashe shi, amma kuma an raunata mutanensa, an kuma yiwa wasu daga ciki yankan Rago, har an samu rasa rai.

Advertisements
Advertisements

Cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin dan majalisar, wasu matasa ne kwance cikin jini a jikkace, yayin da dan majalisar ke tsaya yana ta’ajibin lamarin, yana mai cewa tun a jiyan aka tura takarda Abuja, don a janye masa jami’an tsaro, saboda haka shi akan ran mutum daya, gwara ya hakura da takarar da yake yi ta gwamnan Kano a jam’iyyar APC.

Advertisements

A sakon da ya wallafa, dan majalisar ya bukaci hukumomin tsaro da kuma shugabancin APC na kasa, da suyi bincike domin daukar mataki akan abinda ya faru, wanda hatta zaben ma akwai lam’a a cikinsa, domin an karya dokokin da aka tanada wajen gudanar da zabe, a cewarsa.

Advertisements
Advertisements

Zuwa yanzu dai, gwamnatin jihar Kano bata ce komai akan lamarin ba, ku cigaba da kasancewa da jaridar indaranka domin jin cigaba akan wannan lamari.