News
Yanzu yanzu: Ƙungiyar Malaman Kwalejin Fasaha ta ƙasa (ASUP) ta bada sanarwar janye yajin aikin
Daga kabiru basiru fulatan
Ƙungiyar Malaman Kwalejin Fasaha ta ƙasa (ASUP) ta bada sanarwar janye yajin aikin gargadin da ta shiga makwanni biyu da suka wuce sannan kuma ta umarci ƴaƴan kungiyar nata da su dawo bakin aiki a ranar Litinin mai zuwa 30 ga watan Mayu, na shekarar 2022.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Ƙungiyar Shamma S. Kpanja ya fitar a safiyar yau Asabar.
Majiyar mu ta tuntubi shugaban ƙungiyar reshen Kano State Polytechnic Dakta Muntaka Dahiru inda ya tabbatar mana da maganar komawar a ranar Litinin mai zuwa 30 ga watan Mayun.
Ƙungiyar ta kara da cewa ƴaƴan kungiyar nata su saurari umarni na gaba don gane da yajin aikin bayan babban taro na 103 da Ƙungiyar za ta gabatar a watan Yuni.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
