News
Shaye-shayen miyagun kwayoyi ne ke ta’azzara rashin tsaro a Nijeriya — Ɗan Majalisa
Daga khadija Abdullah muhmd
Wani dan majalisar dokokin jihar Anambra, Dokta Nnamdi Umeh, ya bayyana yawaitar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa a matsayin babban abin da ke ta’azzara rashin tsaro a kasar nan.
Umeh, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin majalisar kan harkokin lafiya, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Awka a yau Talata.
2023: NNPP ta zaɓi Kwankwaso a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa
Ya ce yadda matasa, waɗanda su ne shugabannin gobe suka tsunduma cikin shaye-shayen miyagun kwayoyi abu ne da ke sanya damuwa.
“Rashin zaman lafiya yana dagula al’ummarmu, kuma babu yadda za a yi mu shawo kan lamarin ba tare da magance matsalolin da ke haifar da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasanmu ba.
“Yawancin matasa a yau sun rasa mutunci da kuma mai da hankali, yayin da da yawa suna da ƙalubale na rashin lafiya saboda shan muggan kwayoyi.
“Ba za mu iya dunkule hannu mu yi komai ba, don haka ina so in yi kira ga Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) da sauran masu ruwa da tsaki da su kara wayar da kan matasa kan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi.
“Irin wannan wayar da kan jama’a zai taimaka wa matasa su fahimci cewa babu wanda ke shan miyagun kwayoyi da ke rayuwa cikin nasara.
“Shaye-shayen muggan kwayoyi, ba wai kawai mai amfani da shi ya ke wa illa ba, har da ma iyali da kuma al’umma gaba daya ba. Don haka muna bukatar mu kiyaye makomarsu,” inji shi.
Umeh ya ce kwamitin majalisar kan harkokin lafiya zai hada gwiwa da hukumar NDLEA da sauran hukumomin da abin ya shafa domin dakile matsalar shan miyagun kwayoyi a jihar.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
