News
Bola Tinubu ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na APC
Daga Usman Abdullahi jibirin
Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.
Ya lashe zaɓen ne da ƙuri’a 1,271, kuma dama tun da fari shi ne ƴar manuniya ta nuna ya fi yawan ƙuri’u.
Bisa alƙaluma da aka sanar a bainar jama’a, ministan sufuri Rotimi Amaechi ya samu ƙuri’a 316, yayin da Yemi Osinbajo ya samu ƙuri’a 235.
Shugaban majalisar dattijan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ya samu ƙuri’a 152.
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya samu ƙuri’a 47, shi kuwa tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha bai samu ƙuri’a ko ɗaya ba.
Shi kuwa gwamnan jihar Cross River Ben Ayade ya samu ƙuri’a 37, yayin da gwamnan Ebonyi Dave Umahi ya samu ƙuri’a 38, shi kuwa tsohon gwamnan Zamfara Ahmad Sani Yariman Bakura ya samu ƙuri’a hudu.
Tsohon gwamnan jihar Legas din dai ya mamaye muhawarar shafukan sa da zumuntar a Najeriya kusan mako guda tun kafin zaɓen.
Zaben dai ya ɗauki hankali ƴan Najeriya sosai a ciki da wajen ƙasar, musamman bayan da ƴan takara kusan bakwai suka ce sun janyewa Tinubun.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
