News
Tsohon Ministan Harkokin Ƙasashen Waje ya samu tikitin takarar Sanatan Jigawa a PDP
Daga khadija Abdullah muhmd
Tsohon Ministan ƙasa a Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje, Dakta Nuruddeen Muhammad ya yi nasarar lashe zaben fidda-gwani na takarar sanatan Jigawa ta Gabas a jama’iyyar PDP.
XASUU Ta Yi Watsi Da Tayin Tallafi Don Ta Janye Yajin Aiki
Tsohon Ministan, wanda kuma ya taɓa kula da Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta tarayya ya lashe zaben ne babu hammayya, a wani zaɓen cikin gida na musamman da aka yi a jiya Alhamis a garin Hadejia, da ke jigawa.
Da ya ke jawabin amincewa, ɗan takarar ya godewa dukkanin wakilan jama’iyya da su ka zaɓe shi, inda ya suffanta hakan da karramawa da su ka yi masa.
Ya kuma jawo hankalin al’umma ma su zaɓe da su kaɗa ƙuri’arsu a kakar zaɓe mai zuwa a kan doron tunanin matsalolin da su ke addabarsu.
Ya lissafo matsalolin kamar haka; ambaliyar ruwa, kwararowar hamada, yasar kogin Hadeja da kuma yawaitar ciwon k’oda da dai sauransu, inda ya ci alwashin magance su.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa Muhammad shine wadda yayi wa jama’iyyar PDP takarar mataimakin gwamna a kakar zaben 2015.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
