Connect with us

Sports

Darwin Nunez: Liverpool ta kulla yarjejeniya da Benfica kan dan kasar Uruguay

Published

on

Darwin Nunez

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Darwin Nunez ya ci wa Benfica kwallo a karawar ta da Liverpool inda suka tashi da ci 3-1 da kuma wanda suka yi 3-3 a gasar Zakarun Turai ta kakar da ta wuce

Advertisement

Mun Gano Mutum 29,000 Da Suka Yi Katin Zabe Sau 2 A Kwara — INEC

Liverpool ta kulla yarjejeniya da Benfica domin daukar dan kasar Uruguay, Darwin Nunez, kamar yadda kungiyar ta Portugal ta tabbatar.

Advertisement

 

Benfica ta ce kudin da aka sayi dan wasan sun kai euro 75m (£64m), ko da yake idan aka hada da ‘yan tsarabe-tsarabe kudin za su kai euro 100m (£85m).

Advertisement

 

Nunez, mai shekara 22, ya zura kwallo sau 34 a wasanni 41 da ya fafata wa Benfica a dukkan gasannia kakar da ta wuce.

Advertisement

 

Kudi mafi yawa da Liverpool ta kashe don daukar dan wasan shi nee £75m inda ta biya domin daukar Virgil van Dijk daga Southampton a 2018.

Advertisement

 

Rahotanni sun nuna cewa Manchester United ta so daukar Nunez, wanda Benfica ta sayo daga Almeria a kan euro 24m (£20.5m) a 2020.

Advertisement

 

Dan wasan na gaba, wanda ya ci wa kasarsa Uruguay kwallo 11, ya zura kwallo 26 a gasar lig 28 da ya fafata a kakar 2021-22.

Advertisement

 

Kazalika ya ci kwallo shida a gasar Zakarun Turai 10 da ya fafata a kakar wasan da ta wuce, ciki har da wadanda ya ci Liverpool a matakin kwata fainal a watan Afrilu.

Advertisement

 

Liverpool ta lashe Kofin FA Cup da na Carabao a kakar da ta wuce – sannan ta zo ta biyu a Premier League kana ta sha kashi a wasan karshe na Champions League.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending