Connect with us

Sports

Darwin Nunez: Liverpool ta kammala daukar dan kwallon Uruguay

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Liverpool ta kammala cinikin dan kwallon tawagar Uruguay, Darwin Nunez daga Benfica kan yarjejeniyar kaka shida kan fam miliyan 64.

 

Advertisement

Mai shekara 22 zai zama mafi tsada da kungiyar ta saya a tarihi, idan aka hada da kudin tsarabe-tsarabe da zai kai fam miliyan 85 jumulla.

 

Advertisement

Nunez ya ci kwallo 34 a wasa 41 da ya yi wa Benfica a kakar da aka kammala.

 

Advertisement

Wanda Liverpool ta dauka da kudi da yawa a tarihi, shi ne Virgil van Dijk, kan fam miliyan 75 daga Southampton a 2018.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kudin da aka sayo Nunez zai karu zuwa fam miliyan 85, idan har zai ke buga wasa a koda yaushe.

 

Advertisement

Kudin karin tsarabe-tsarabe ya kunshi kwallo nawa zai ci da idan Liverpool ta dauki Champions League.

 

Advertisement

Komawar dan kwallon zuwa Liverpool ya danganci samun takardar izinin taka leda a Ingila.

 

Advertisement

Nunez, wanda ya ci wa Uruguay kwallo 11, ya zura 26 a raga a karawa 28 a babbar gasar tamaula a Portugal a 2021-22 – guda 25 da ya ci da shi aka fara wasa.

 

Advertisement

Ya kuma ci shida a fafatawa 10 a Champions League da aka karkare, har da wadanda ya zura a ragar Liverpool a karawa gida da waje a kwata fainals cikin watan Afirilu.

 

Advertisement

Liverpool ta lashe Carabao Cup da FA Cup a kakar da ta kare ta kuma yi ta biyu a Champions League, bayan da Real Madrid ta dauki na 14 jumulla.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending