Connect with us

News

An soma kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamna a Ekiti

Published

on

An soma tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma dangwala ƙuri’a a wasu rumfunan zaɓe tun da misalin 8:30 na safe.

Wasu daga cikin rumfunan zaɓen da wakilan BBC suka ziyarta a Ado-Ekiti musamman mazaɓar Oke-Inyimi, tuni aka fara zaɓe a rumfa mai lamba biyu da mai lamba uku da huɗu da shida.

Owolabi Comfort ita ce mace ta farko da ta soma zaɓe a rumfa mai lamba biyu.

Ana amfani da sabuwar na’urar Bvas wurin tantance masu zaɓen.

Na’urar Bvas wato Bimodal Voter Accreditation system, an soma amfani da ita ne a zaɓen gwamna a Anambra a 2021 duk da cewa an samu tangarɗa a wasu wuraren.

Sai dai a zaɓen Ekiti, hukumar ta INEC ta ce za sake inganta na’urar ta Bvas inda ta ce tana sa ran za ta yi aiki da kyau.

Advertisement

8:30 na safe za a soma zaɓe da tantance ƴan takara a Ekiti – INEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC wadda ita ce alhakin zaɓe a Najeriya ya rataya a wuyanta ta ce za a soma tantance ƴan takara da kuma gudanar da zaɓe da misalin 8:30 na safe a kuma a kammala 2:30 na rana.

Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter inda ta ce duk wanda ya bi layin zaɓen kafin 2:30 na rana za a bar shi ya dangwala.

Jami’an INEC sun isa rumfunan zaɓe da wuri’

Wasu daga cikin mazauna Jihar Ekiti sun soma fita zuwa rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar.

Tun ƙarfe 7:15 na safe jami’an hukumar INEC suka soma isa rumfunan zaɓe a Ado-Ekiti babban birnin jihar.

Wannan na zuwa ne bayan INEC ɗin ta kammala rarraba kayayyakin zaɓe tun da misalin ƙarfe 3:00 na asuba.

Wasu daga cikin masu zaɓen sun shaida wa BBC cewa jami’an na INEC waɗanda akasarinsu masu yi wa ƙasa hidima ne na NYSC sun isa wuraren zaɓen da wuri.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending