Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC wadda ita ce alhakin zaɓe a Najeriya ya rataya a wuyanta ta ce za a soma tantance ƴan takara da kuma gudanar da zaɓe da misalin 8:30 na safe a kuma a kammala 2:30 na rana.
Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter inda ta ce duk wanda ya bi layin zaɓen kafin 2:30 na rana za a bar shi ya dangwala.
Jami’an INEC sun isa rumfunan zaɓe da wuri’
Wasu daga cikin mazauna Jihar Ekiti sun soma fita zuwa rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar.
Tun ƙarfe 7:15 na safe jami’an hukumar INEC suka soma isa rumfunan zaɓe a Ado-Ekiti babban birnin jihar.
Wannan na zuwa ne bayan INEC ɗin ta kammala rarraba kayayyakin zaɓe tun da misalin ƙarfe 3:00 na asuba.
Wasu daga cikin masu zaɓen sun shaida wa BBC cewa jami’an na INEC waɗanda akasarinsu masu yi wa ƙasa hidima ne na NYSC sun isa wuraren zaɓen da wuri.
