Connect with us

News

Gwamnan Zamfara Matawalle ya bai wa ma’aikata hutun mako ɗaya don su yi rajistar zaɓe

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

 

 

 

Gwamnatin Jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta bai wa ma’aikatan jihar hutun mako ɗaya domin su yi rajistar katin zaɓe da ake gudanarwa yanzu haka a faɗin ƙasar.

Ɗan damfara da yaudara a facebook, wanda ke nuna kansa a matsayin Zahra Mansur ya shiga hannu

Advertisement

Matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamashinan Yaɗa Labarai na Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar a yau Asabar.

 

Ya ce Gwamna Bello Matawalle ya amince da ba da hutun ne daga Litinin, 20 zuwa 24 ga watan Yuni.

 

“Sakamakon wannan sanarwa, an umarci dukkan kwamashinoni da masu bai wa gwamna shawara da sakatarori da sauran ma’aikatan gwamnati da jami’an jam’iyyun siyasa da su saka ido kan yadda aikin rajistar ke tafiya,” a cewar kwamashinan.

 

Advertisement

Ƙungiyoyi da ‘yan gwagwarmaya a Najeriya na ci gaba da kira ga hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da ta tsawaita wa’adin yin rajistar, suna masu cewa mutane da dama ba su samu damar yi ba saboda ƙarancin kayan aiki da kuma cunkoso.

 

INEC ta saka ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar ƙarshe da za a rufe aikin rajistar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending