News
Sabon gwamna da aka zaɓa a Ekiti ya ziyarci Buhari
Daga Hamza Yusuf Abdulmumin
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakwacin sabon gwamna da aka zaba a Ekiti, Biodun Oyebanji, a fadarsa da ke Abuja.
Zababben gwamnan ya ziyarci shugaba Buhari da rakiyar wasu gwamnonin jihohin Najeriya da wasu ‘ya’yan Jam’iyyar da suka taimaka wajen kai wa ga nasararsa a zaben.
A daren Asabar hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta bayyana Biodun Abayomi Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ekiti.
INEC ta ce Mista Oyebanji ya samu kuri’u 178,057.
Hakan ya sanya jam’iyyar All Progressive Congress ta zamo wadda ta samu kuri’u mafi yawa a zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Yunin shekara ta 2022.
Dan takarar jam’iyyar Social Democratic Party, Olusegun Oni, shi ne ya zo na biyu a zaben inda ya samu kuri’u 82,211.
Sai jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) wadda ta zo ta uku, inda dan takararta Bisi Kolawole ya samu kuri’u 67,457.
Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar APC ce ta lashe kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar, inda jam’iyyar PDP ta yi nasara a karamar hukuma daya tal.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
