Sports
Mane yaje jamus Dan kammala komawar sa beyern munich
Daga kabiru basiru fulatan
Sadio Mane ya je birnin Munich ranar Talata, don kammala komawa Bayern Munich da taka leda daga Liverpol.
Sky ta saka wani faifan bidiyon dan kwallon a wani jirgi na kawa da ya isa birnin a shirin auna koshin lafiyar dan wasan tawagar Senegal.
Bayan auna koshin lafiyar dan wasan zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku, inda mujallar Kicker sports ta ce za a gabatar da dan kwallon a ranar Laraba.
Mane zai koma buga Bundesliga kan yuro miliyan 32, ana cewa kudin zai kai yuro miliyan 41 idan aka hada da tsarabe-tsarabe.
Dan kwallon tawagar Senegal zai karfafa wasannin Bayern Munich, bayan da ake cewar ba a san makomar Serge Gnabry, sannan Robert Lewandowski na san zuwa Barcelona a kakar da za a fara a badi.
Sau biyu Liverpool tana yin watsi da tayin da Bayern ta yi mata kafin ta amince ta sayar da dan wasan mai shekara 30, wanda kwantaraginsa da Reds za ta kare a bazara.
Liverpool ta saye shi daga Southampton a shekarar 2016 a kan £31m da karin £2.5m na tsarabe-tsarabe.
Tun daga wancan lokacin, Mane ya zura kwallaye 90 a Gasar Firimiya a wasannin da ya yi wa kungiyar sannan ya kammala kakar wasan da ta wuce da cin kwallaye 23 a gasa daban-daban da ya yiwa Liverpool
-
News7 days ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News4 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News3 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
