Sports
NPFL: Pillars ta doke Dakkada FC a kwantan wasan mako na 31
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasarar doke Dakkada FC da ci 1 mai ban haushi a gasar cin kofin Firimiya ta Najeriya a kwantan wasan mako na 31.
Dan wasan tsakiya na kungiyar ta Kano Pillars Yusuf Bala Maigoro ne ya zura kwallon data bawa Pillars Nasara a minti na 22 da fara wasa.
An dai buga wasan ne a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata.
Da wannan sakamakon yanzu haka Pillars na matakin ta 15 da maki 42 a teburin gasar ta shekarar 2021/2022.
Kafin wannan wasa dai Pillars na a matsayin ta 19 a gasar Firimiyar ta Najeriya
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana



