News
Yan nijeriya 38 Sun Mutu Wajen Taimaka Wa Ukraine A Yaki inji Rasha
Daga Yasir sani Abdullahi
‘Yan Najeriya 38 Sun Mutu Wajen Taimaka Wa Ukraine A Yaki inji Rasha
‘Yan Najeriya 38 da ke taimaka wa Ukraine a yakin da take da mamayar Rasha ne suka mutu a fagen daga, a cewar wani kundi da ma’aikatar tsaron Rasha ta wallafa, wanda ke dauke da adadin sojojin haya da suka mutu.
‘Yan Najeriya 38 daga cikin 85 da suka je taimaka wa Ukraine ne suka mutu, a yayin da 35 suka koma gida, 12 na nan suna ci gaba da yaki a matsayin sojojin haya.
Wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron ta Rasha ta ce duk kuwa da dimbim kudade da gwamnatin Ukraine ke biyan sojojin hayan hakan bai hana dakarun Rasha aika su barzahun ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa tun da aka raba rana tsakanin Rasha da Ukraine, mutane dubu 1 da dari 8 da 31 suka isa kasar daga Poland kawai da zummar yin aiki a mstayin sojojin haya, inda daga cikin su, 378 sun kwanta dama, a yayin da 272 suka arce zuwa kasashensu na asali.
A cewar ma’aikatar tsaron ta Rasha, akwai sojojin haya dubu 3 da 321 da ke da rai, wadanda ba a kai ga kame su ba, ko kuma ba a kashe ba, tana mai cewa daga ranar 17 ga watan Yuni, mayaka ‘yan kasashen waje dubu 1 da dari 956 ne Rasha ta kashe, a yayin da sama da dubu 1 da 700 suka arce zuwa kasashensu.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
