Connect with us

News

ISWAP ta yi iƙirarin kashe dakarun Najeriya uku a Jihar Borno

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

ISWAP ta yi iƙirarin kashe dakarun Najeriya uku a Jihar Borno

Ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) mai iƙirarin jihadi ta yi iƙirarin cewa ta kashe mayaƙan sa-kai uku da ke aiki da rundunar sojan Najeriya a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Kazalika, ta ce ta yi garkuwa da wasu ma’aikatan agaji na ƙungiyar Red Cross yayin harin da ta ce ta kai ranar Juma’a.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne ciikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na dandalin Telegram, tana mai cewa ta kai harin ne a garin Monguno.

Sai dai ƙungiyar kan kira wasu mutane da ta kama da cewa ma’aikatan Red Cross ne ko da kuwa ba natan ba ne.

Advertisement
  1. A watan Agustan 2020 ne ƙungiyar ta ayyana yaƙi a kan ma’aikatan agaji da ke aiki a Jihar ta Borno, tana mai zargin su da aiwatar da ayyukan abinda suka kira “rusa Musulunci”.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending