News
Janar abdussalam abubakar ya Sami sauki zai dawo kasa nigeria a kwanannan
Daga Yasir sani Abdullahi
Janar Abdussalami Abubakar ya samu sauki zai dawo gida NIGERIA a kwanan nan.
Tsohon shugaban mulkin sojin NIGERIA Janar Abdussalami Abubakar ya samu sauki zai dawo gida NIGERIA a kwanan nan ba da jimawa ba – Inji Garba Shehu
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu shine ya bayyana hakan ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewar sa ya gana da Abdussalam a birnin London inda ya ke jinya Kuma tuni jiki yayi kyau har ma ya tambayeshi halin da NIGERIA ke ciki.
A baya-bayan nan ne dai janar Abdussalami Abubakar ya tafi birnin London domin ganin likita sakamakon rashin lafiya da ya ke fama dashi.
Advertisements
