News
Yan Najeriya na kokawa kan matsananciyar tsadar man diesel a arewacin kasar
Daga Usman Abdullahi jibirin
Masu masana’antu a Najeriya na ci gaba da kokawa kan matsananciyar tsadar man diesel, inda a yanzu farashin litar ya zarce Naira dari takwas. Masu masana’antun na kokawa ne bayan da kungiyar masu hada-hadar man diesel a kasar suka yi hasashen cewar kowace litar mai na iya kaiwa Naira dubu da dari biyar nan gaba kadan.
A cikin wannan shekara ce Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke kare matakin da gwamnatin sa ta dauka na bijirewa shawarar Hukumar Bada Lamuni ta Duniya wato IMF wajen cire tallafin man fetur a kasar, ya ce halin da wasu kasashe suka tsinci kan su sakamakon cire tallafin man fetur, izina ce ga Najeriya.
Wakilinmu na Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo ya yi nazari game da wannan batu ga kuma rahoton da ya aiko mana.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
