Connect with us

News

Buba Marwa ya na neman tona asirin ‘Yan siyasa, NDLEA ta cafke masu harkar kwayoyi. 

Published

on

NDLEA

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban hukumar NDLEA mai yaki da masu amfani da safarar miyagu na kasa, Buba Marwa, ya ce sun damke wasu ‘yan siyasa da kwayoyi.

Dalibai 29,000 Muka Biya Wa Kudin NECO A Bana — Gwamnatin Kano 

Advertisement

Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV, inda ya tabbatar wa da Duniya cewa NDLEA ta yi ram da ‘yan siyasa da kwayoyi.

 

Advertisement

Kamar yadda aka fitar da rahoto a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni 2022, Buba Marwa ya nuna takaicinsa a game da yadda ya samu cikas a wajen aikinsa.

 

Advertisement

Shugaban hukumar NDLEA yake cewa bai yi nasara a yunkurin da ya nemi ya kawo na ganin an yi wa duk jami’in gwamnati gwaji kafin ya shiga ofis ba. NDLEA ta yi koyi da Kano A cewar Janar Marwa, NDLEA ta aro wannan tsaro ne daga jihar Kano, inda ake yi wa duk wasu ‘yan APC gwajin kwayoyi kafin a ba su mukami a gwamnati.

 

Advertisement

Mun kama ‘yan siyasan da ko su na rike da mukamai a yanzu, ko sun yi ritaya.

 

Advertisement

Kwanan nan aka daure wani daga cikinsu a gidan yari a Legas

 

Advertisement

“An daure shi yana kokarin ya yi safarar kilo daya.

 

Advertisement

Watakila zai yi amfani da shi wajen takara.” “Kamar yadda ku ka sani, masu dillacin kwayoyi su na shiga siyasa, su na ba ‘yan takara gudumuwa domin a taba doka idan sun ci zabe.”

 

Advertisement

Da yake bayanin yadda kula da tsofaffin ‘yan kwaya, The Cable ta rahoto Marwa yana cewa duk wuraren kula da tubabbun mashaya kwaya sun lalace.

 

Advertisement

A cewarsa, akwai dinbin mutane da ke so su daina wannan muguwar harkar, amma sun gagara.

 

Advertisement

Marwa ya ce a halin yanzu cibiyoyi 11 rak ake da su na kula da wadanda suke neman yin ban kwana da miyagun kwayoyi, a maimakon uku a duk jiha.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending