News
Mun ceto rayuka 135 da dukiya ta N34.6 m a wata guda — Hukumar Kwana-kwana ta Kano
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta ce ta ceto rayukan mutane aƙalla 135 da kuma dukiyoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 34.6 daga aukuwar gobara 42 a watan Yunin da ya gabata.
Ba zan yadda na zama mataimakin ɗan takara ga kowa ba — Kwankwaso
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi da ya fitar a yau Lahadi a Kano.
Abdullahi ya ce, mutane 24 ne suka mutu, sannan an kiyasta asarar dukiya ta Naira miliyan 13 da gobarar ta yi a lokacin.
A cewar sa, ma’aikatar ta amsa kiraye-kirayen ceto 77 da kuma kararrawar karya 17 daga mazauna jihar.
Kakakin ya danganta tashin gobarar da na’urorin lantarki marasa inganci da rashin kulawa.
Ya shawarci jama’a da su rika kulawa sosai don gujewa tashin gobara, yayin da bukukuwan Sallah ke gabatowa.
Abdullahi ya kuma bukace su da su rika bin dokokin hanya domin gujewa hadurran mota yayin bikin.
