News
Hukumomin Saudiyya sun kara wa’adin saukar jirage ga maniyyatan Najeriya
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Saudiyya ta kara wa’adin saukar jirage ga mahajjatan Najeriya daga 4 zuwa 6 ga watan Yuli
An ƙara samun wani matashin wuta ta ja shi ya mutu yayin sata a taransifoma
Mataimakiyar daraktan kula da harkokin yada labarai na hukumar alhazan Najeriya Hajiya Fatima Usara ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a Abuja.
Ta kara da cewa kara wa’adin ya zama wajibi ne sakamakon yawan jiragen da aka soke tashinsu da kuma wadanda aka samu jinkiri wajen tashinsu
Ta kara da cewa hakan ya faru ne sakamakon wasu dalilai da suka hada da kasa samar wa maniyya kudin guzuri da wasu hukumomin alhazai na jihohi suka yi, da rashin wadatattun kudin biza, tare da gaza samun sakamakon gwajin Korona da aka yi wa maniyyatan a kan lokaci.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
