News
Na ji takaici ga tsarin tsaron sirri na ƙasar nan -Buhari
Daga kabiru basiru fulatan
A yau Laraba ne dai Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan yarin Kuje da ƴan ta’adda su ka kai wa hari, inda ya nuna rashin jin dadinsa da tsarin tsaron sirri na kasar nan.
Bayan duba illar da harin ya yi, Buhari ya zanta da manema labarai, inda ya nuna rashin jin dadinsa ga tsarin tsaron sirri na ƙasar nan da kuma yadda a ke gudanar da shi.
Dukkan ‘yan Boko Haram din da ke daure a Kuje sun tsere — Minista
Ya ce: “Na ji takaici ga tsarin tsaron sirri na ƙasar nan. Ta yaya ƴan ta’adda za su iya shiryawa tare da ɗaukar makamai, su kai hari a kan cibiyar tsaro kuma su tafi salin-alin?”
Shugaban, wanda kamar yadda akasarin ’yan Najeriya, ya nuna kaɗuwarsa ga irin girman harin, inda yayi tambaya “ yaya aka yi jami’an tsaron gidan yarin suka kasa daƙile harin? Fursunoni nawa ne ke cikin gidan yarin?
“Nawa ne za ku iya lissafowa? Ma’aikata nawa ne ke da su a bakin aiki? Nawa ne a cikinsu ke ɗauke da makamai? Akwai masu gadi a hasumiyar tsaro? Me suka yi? Shin kyamarar CCTV tana aiki?” Tambaya bayan tambaya.
An kuma sanar da Shugaban kasar, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Senegal, cewa, jami’an tsaro sun kamk fursunoni 350 daga cikin wadanda suka tsere, yayin da wasu kimanin 450 ba a san inda su ke ba, kuma ana ci gaba da aikin nemo sauran.
Buhari, tare da rakiyar Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, ya ce a karshen ziyarar yana sa ran samun cikakken rahoto kan lamarin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
