News
Karancin man Fetur a Kamaru ya tilasta wa kungiyar direbobi jingine ayyukanta
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Shugaban kungiyar direbobin motocin haya a Kamaru Ibrahim Yaya, ya ce karancin man fetur ya tilasta wa ‘ya’yan kungiyar jingine ayyukansu.
A wata sanarwa da Ministan makamashin kasar ya fitar ranar Litinin ya yi alkawarin kawo man cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Mista Essomba ya yi bayanin cewa karancin man ya faru ne sakakamon karuwar kudin tallafin man da gwamnati ke biya saboda tashin farashin man a kasuwar duniya.
Inda ya ce gwamnati na bukatar isasshen lokaci domin tara kudin da za ta iya biyan tallafin.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
