News
Tsadar rayuwa ta yi tsanani a Ghana
Daga Maryam bashir musa
‘Yan Ghana sun yi zanga-zangar tsadar rayuwa a watan da ya wuceImage caption: ‘Yan Ghana sun yi zanga-zangar tsadar rayuwa a watan da ya wuce
Hauhawar farashin kaya da aiki a Ghana ta kai kashi 29.8 cikin dari a watan Yuni tun watan Disamba na 2003.
Babu gadon dana barwa yara na idan na sauka daga mulki sai ingataccen ilimi, -cewar Shugaba Buhari
Ofishin kididdiga na kasar ya ce hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayayyaki na masarufi su ne ke janyo tashin.
Yanzu gwamnatin kasar ta karkata ga Asusun bayar da lamuni na duniya, (IMF) domin samun tallafin da ya kai na dala miliyan 1.5, kwatankwacin fam biliyan 1.3
Idan har Asusun ya amince, to wannan zai kasance karo na 17 da kasar ta Ghana ke rance kudi daga wurinsa IMF din tun bayan da ta samu ‘yancin-kai a 1957.
Ana kiyasin bashin da ake bin kasar gaba daya ya kai sama da kashi biyu bisa uku na kudin da take samu.
Kuma karuwar bashin ka iya zama illa ga al’ummar kasar ta gaba, sannan zai tsoratar da ‘yan kasuwa masu zuba jari.
Masana tattalin arziki sun yi amanna yin sauye-sauye a kan harkokin kashe kudi, kamar albashi da basukan cikin gida da rage tallafi da kudaden da gwamnati ke kashewa, duka wadannan ka iya rage tsananin matsalar.
Ana sa ran ministan kudi zai gabatar da bayani kan kasafin kudi na tsakiyar shekara a gaban majalisar dokokin kasar a watan nan na Yuli.
