Connect with us

News

Sayar da litar man fetur kan N165 ba abu ba ne tabbatacce — MOMAN

Published

on

Daga mujahid danlami garba 

 

 

Kungiyar Manyan Dillalan Mai ta Ƙasa, MOMAN, ta ce kayyade farashin litar man fetur kan N165 ba tabbataccen abu ba ne.

 

Olumide Adeosun, Shugaban MOMAN, ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin wani taron karawa juna sani na kariya ga masu siyan mai da Hukumar Kare Cinikayya da Sayen ta Tarayya, FCCPC.

Advertisement

Tsadar rayuwa ta yi tsanani a Ghana

Adeosun, wanda ke tsokaci kan matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a fadin kasar, ya ɗora alhakin lamarin kan rikicin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine, wanda ya kawo cikas ga rarraba makamashi a faɗin duniya.

 

Shugaban MOMAN ya kwatanta halin da ake ciki a halin yanzu da na lokacin annobar COVID-19, inda wasu kasashe suka yi yunkurin dakatar da fitar da man fetur zuwa kasashensu na samar da makamashi na kasa.

 

Ya ci gaba da cewa zai yi wahala a tilasta duk wani nau’in tsarin kula da farashi a kan ‘yan kasuwa, wadanda sai da su ka yi hoɓɓasar daidaita farashinsu dangane da yadda suke siyan kayayyakin daga rumbunan mai.

Advertisement

 

Shugaban MOMAN ya ce hanyar da za a bi ita ce gwamnati ta gaggauta ɗaukan matakin janye tallafin mai domin a sauƙaƙa wa masu sayen a ƙasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending