Connect with us

News

An saka dokar hana fita a wasu garuruwa biyu na Sudan

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

An saka dokar hana fitar dare a wasu garuruwa biyu na kasar Sudan, bayan artabu na tsawon kwanaki tsakanin wasu kabilu wanda ya jawo mutuwar aƙalla mutum 31 da jikkata gwammai.

An aike da sojoji zuwa yankin domin kwantar da tarzomar da ta ɓarke kan rikicin filaye tsakanin kabilun Berti da kuma Hausawan da ke kudu maso gabashin Jihar Blue Nile.

Ma’aikacin Filin Jirgi Ya Saci Jirgin Sama

Rikicin ya ɗaiɗaita gwamman mutane da kuma sanadin ƙona shaguna da dama yayin artabun da aka soma tun ranar Litinin.

Duk da sanya dokar hana fitar daren, rahotanni na nuna cewa ana ci gaba da gwabza fada a daya daga cikin garuruwan mai suna Roseires .

Advertisement

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Sudan, ya kira ga al’ummomin da su kai zuciya nesa.

. Source bbc 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending