Connect with us

News

An sake gano wata ‘yar Chibok a Borno

Published

on

DAGA MUJAHID DANLAMI GARBA

 

 

Advertisement

 

Dakarun soji na rundunar Hadin kai, da ke yaki da Boko Haram a Najeriya, sun tabbatar da sake gano wata ‘yar makarantar Chibok mai suna Ruth Bitrus, wacce ta kubuta daga hannun mayakan Boko Haram tare da danta.

Advertisement

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito babban kwamandan dakarun rundunar, Manjor janar GC Musa na bayyana hakan ranar Laraba.

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibin jami’a

Advertisement

A lokacin da yake mika wasu magunguna da hukumar raya yankin arewa maso gabas ta bai wa sojojin da ke aiki a yankin.

Kwamandan ya ce ”Idan za ku iya tunawa makonni da suka gabata, mun kubutar da ‘yan matan Chibok biyu, to yanzu ma mun sake kubutar da wata guda daya”

Advertisement

A ‘yan kwanakin baya ne dai, dakarun suka kubutar da ‘yan mata biyu a karamar hukumar Gazuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending