Connect with us

Uncategorized

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Za Ta Rushe Makarantun Kwana Domin Hana Kai Hare-hare A Makarantu

Published

on

Daga Yasir sani Abdullahi

Gwamnatin Tarayya na shirin ajiye wasu sabbin matakai na magance aikace-aikacen ƴan ta’adda da ƴan bindiga daga gudanar da mummunan ta’addancin su a makarantu.

Babban Sakataren Ma’aikatar Ilmi na Kasa Mr. Andrew David Adejo ya bayyana haka a lokacin taron Kwamitin tuntuɓa na Ilmi karo na 81 daya gudana a ɗakin taro na Banquet dake gidan Gwamnatin Jahar Adamawa a ranar Litinin.

Mr. Adejo ya bayyana cewar wasu daga cikin matakan sun ƙunshi, shigo da malamai da ɗalibai akan harkokin tsaro, da rushe makarantun kwana, da ƙirƙirar ɓangaren tsaro na musamman a makarantu, da sanya na’urorin ɗaukar hoto na CCTV, da ɓullo da darasi akan tsaro na manyan makarantu.

“Ya zama dole yadda ake samun kai hare-hare a makarantun ilmin mu, sace i, da iyaye, wanda hakan na kawo tsaiko ga ɓangaren ilmi.

Yace taken taron wannan shekarar shine “inganta tsari da kare makarantun najeriya domin cimma nasarori da aka tsara zuwa shekarar 2030” nada manufar inganta koyo, tare da magance Ɗabi’a da halaye da lafiyar Makarantu.

Advertisement

Gwamnan Jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda ya buɗe taron, yace gwamnatin jahar tuni ta gano yadda mahimmancin canja yanayin tsarin makarantu a jahar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending