Connect with us

News

Muna ƙarancin wurin ajiye tubabbun ‘yan Boko Haram – Sojin Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Hukumomi a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, sun ce sun fara rasa wuraren da za su ajiye mayaƙan Boko Haram da suka miƙa wuya.

 

Advertisement

Babban jami’in soja Manjo Janar Chris Musa ya ce a yayin da miƙa wuyan da mayaƙan Boko Haram ɗin ke yi yake taimakawa wajen shawo kan rikicin da ya addabi yankin, a gefe guda kuma babu isassun wuraren ajiye su.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe N30bn Don Gyaran Majalisa

Babban janar ɗin ya ce zuwa yanzu akwai mayaƙan da suka yi saranda kuma suke jiran bin matakan sauya musu tunani, amma ba su da wajen ajiye su.

 

Wuraren ajiye mutanen sun cika maƙil – kuma a yanzu hukumomi suna duba yiwuwar gina wasu.

 

Advertisement

Matakan sauyawa da gyara tunani na cikin ƙoƙarin da gwamnatin Najeriya ke yi don kawo ƙarshen ayyukan masu iƙirarin jihadi, musamman a arewa maso gabashin ƙasar.

 

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa kusan mutum 350,000 ne suka mutu a rikici tsakanin ƙungiyar Boko Haram da rundunar sojin ƙasar cikin shekara 12. Amma adadin ka iya fin haka.

 

Janar Chris Musa ya ce wani babban ƙalubalen shi ne yadda suke samun matsalar mayar da ƴan gudun hijira matsugunansu.

 

Advertisement

Hakan na faruwa ne sakamakon ƴan tayar da ƙayar bayan sun daddasa nakiyoyi a kan hanya.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending