News
Yan bindiga sun kashe direba tare dayin garkuwa da wasu
Daga Yasir sani Abdullahi
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani direba dake aiki da kamfanin sufuri na jihar Katsina.
Direban mai suna Nasiru Yusha’u ya mutu ne bayan bude musu wuta da ‘yan bindigar suka yi akan titin Katsina zuwa Jibiya.
Rahotanni na nuni da cewa tuni ‘yan bindigar suka yi garkuwa da fasinjojin motar direban da suka kashe.
Wasu mazauna kauyen Daddara dake kusa da inda ‘yan bindigar suka yi ta’addancin sun bayyana cewa harin ya faru ne da tsakar ranar jiya Lahadi.
Sun kara da cewa direban yayi kokarin juya kan motar don tsira daga hadarin ‘yan bindigar, inda kokarin nasa bai yi nasara ba har suka cimma masa, inda suka kashe shi nan take.a gurin
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
