News
Jihohin Legas da Kano ne kan gaba a yawan sabbin masu rajistar zabe – INEC
Daga muhammad muhammad zahraddin
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta ce an samu sabbin masu rajistar zabe sama da miliyan 11 da suka yi rajistar a fadin kasar.
Alkaluman da hukumar ta fitar a shafinta na Tuwita sun nuna cewa mutum miliyan 11,011,119 ne suka kammala rajistar a lokacin da ta wallafa sakon.
Dawowar Messi zuwa Barcelona ba abu ne mai yiwuwa ba yanzu
Alkaluman sun kuma nuna cewa jihar Legas ce kan gaba a yawan wadanda suka yi rajistar, inda take da mutum 508,936, sai kuma jihar Kano da aka samu sabbin masu rajistar zaben 500,207, sai Delta mai 481,929, sai kuma jihohin Rivers da Kaduna da ke matsayi na hudu da na biyar
Alkaluman sun kuma nuna cewa matasa ne masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34, suka fi yin rajistar zaben
Sannan kuma alkaluman sun nuna cewa mata sun fi maza yin rajistar, inda aka samu mata miliyan 5,558,048, fiye da adadin maza miliyan 5,453,071 da suka yi rajistar.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
