Connect with us

News

Sanatoci Najeriya sun fice daga zauren majalisa a fusace kan kudurin tsige Buhari

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Sanatocin Najeriya na jam’iyyun adawa sun fice daga zauren majalisar dattawan a fusace, bayan da aka yi watsi da kudurin da suka gabatar na tsige Shugaba Buhari.

 

Advertisement

Gidan Talbijin na Channels TV na ƙasar ya ruwaito cewa ‘yan majalisar na jam’iyyun adawa sun bai wa shugaban kasar Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida da ya kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fama da ita.

Ganduje zai miƙa sunayen sabbin kwamishinoni gaban majalisar dokoki domin tantance wa

Advertisement

Sun kuma yi barazanar fara batun tsige shugaban matukar ya kasa magance matsalar cikin wa’adin da suka ba shi.

 

Advertisement

Shugaban marasa rinjaye na majalaisar, Sanata Phillip Aduda ne ya gabatar da kududrin a gaban zauren majalisar, inda ya roki shugaban majalisar Ahmed Lawan da ya amince majalisar ta tattauna batun tsaro, da kuma na tsige shugaban kasar.

 

Advertisement

To amma shugaban majalisar dattawan ya ƙi amincewa da bukatar dan majalisar yana mai cewa sam-sam ƙudirin bai dace ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending