Connect with us

News

Farashin tikitin jiragen sama ya tashi sosai a Najeriya

Published

on

Daga muhammad muhammad zahraddin

 

 

 

Farashin tikitin jiragen sama a Najeriya ya yi tashin gwauron-zabi yayin da kamfanonin zirga-zirga ke fama da tsadar man jirgi da kuma faɗuwar darajar naira.

 

Advertisement

Bayanai a ranar Juma’a sun nuna cewa farashin tikitin jirgi na Azman Air daga Legas zuwa Kano da Kaduna ya tashi daga kamar N60,000 zuwa N100,000.

Kotun majistre ta umarci matashi da ya share haraba bisa yunƙurin yin sata

Shi ma kamfanin Max Air ya ƙara farashin zuwa Kano daga Abuja zuwa N79,000 mafi ƙaranci.

 

Shi ma kamfanin Air Peace ya ce farashin tikitinsa daga Legas zuwa Abuja ya koma N80,000, komawa kuma N85,000.

 

Advertisement

Ibom Air ma ya mayar da farashin zuwa N80,000 daga Legas zuwa Abuja, yayin da za a biya N130,000 a Max Air kan tikitin Fatakwal zuwa Kano.

 

Yayin wata ganawa da suka yi da Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika a ranar Talata, ƙungiyar masu zirga-zirgar jiragen ta koka kan farashin man jirgin na jet A1 da suka ce ya kai kusan N100 kan kowace lita ɗaya.

 

Duka wannan na faruwa ne baya ga tsaiko na tsawon awanni da fasinjoji ke fuskanta a filin jirgi kafin tashinsa a mafi yawan lokaci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending