Gwamnatin Najeriya ta kashe naira tiriliyan biyu wajen biyan kuɗin tallafin man fetur cikin wata shida na shekarar 2022, a cewar rahoton kamfanin mai na ƙasar NNPC.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa a ranar Tala ne NNPC ya gabatar da rahoton ga kwamatin asusun kasafi na ƙasa wato Federation Accounts Allocation Committee (FAAC).
Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 164 a Najeriya a 2022
Saboda ƙarin yawan kuɗin da ake biya na tallafin ya sa NNPC bai bai wa gwamnatin ƙasar ko kwandala ba a matsayin riba cikin shekarar nan, a cewar rahoton.
A shekarar da ta wuce, gwamnati na biyan naira biliyan 100 ne duk wata a matsayin kuɗin tallafi. Shugabannin kamfanin ba su ce komai ba lokacin da Reuters ya nemi ƙarin bayani.
A watan Janairu ne ya kamata ƙasar ta dakatar da biyan tallafi amma sai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ɗage matakin, tana mai cewa nauyin zai yi wa ‘yan ƙasa yawa yayin da ake fama da hauhawar farashi.
Najeriya na shigar da dukkan man fetur ɗin da ake amfani da shi a ƙasar saboda
